Sansanin Horo na Shirin Gasar Buge-Buge Bootcamp

Our Blog

Sansanin Horo na Shirin Gasar Buge-Buge Bootcamp

Sansanin Horo na Shirin Gasar Buge-Buge Bootcamp

Bayan kammala tantancewa a jihohin Sokoto, Katsina da Zamfara, zaƙakuran matasan da aka zaɓo domin shirin sun isa sansanin horo.
Waɗannan matasa, na daga cikin masu hazaka da ƙwarewa a harkokin kasuwanci a Arewa maso Yammacin Najeriya, za a basu horo na musamman domin bunƙasa ƙwarewarsu.
Shirin Buge-Buge Bootcamp, wanda Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta ɗauki nauyi, sannan ƙungiyar Search for Common Ground Nigeria ke aiwatarwa, da manufar sauya yunƙurin matasa zuwa ingantattun hanyoyin dabarun kasuwanci da inganta zaman lafiya tare da shirya su don fitowa cikin ƙwarewa a shirin gasar ta talabijin.

Domin shirya mahalarta gasar da kuma fafatawa yadda ya kamata, wurin faɗaɗa kasuwancinsu da kuma jagorantar al’umma, sansanin horon ya tanadi cikakken tsarin karatu da horo na kwanaki takwas.
A wannan lokacin, mahalartan za su samu horo kan Hanyar Gina Fahimtar Juna (CGA) da hanyoyin sauya rikice-rikice zuwa zaman lafiya; dabarun sadarwa, mu’amala da kafafen yaɗa labarai da gina zaman lafiya ta hanyar fasahar zamani; wayar da kai kan tsaron kai, kiyaye fasaha da na kasuwanci; kariya daga cin zarafi da cin zarafin jima’i (PSEAH), matakan kariya (Safeguarding) da fahimtar tasirin raunin da rikice-rikice ke haifarwa (Trauma Awareness); hanyoyin magance tsattsauran ra’ayi (P/CVE); da kuma manyan darussa kan harkokin kasuwanci, sarrafa kuɗi, adana bayanan kasuwanci da bin dokokin haraji, da sauran wasu muhimman fannoni.

An ƙaddamar da wannan muhimmin shiri bisa halartar manyan baƙi, da su ka hadar da Shugaban Tawagar Yankin Afirka ta Yamma da Tafkin Chadi na Hukumar Tarayyar Turai (EU) Francesco Carboni sai Muhammad Auwal Aminu, daga Cibiyar da ke Yaki da Ta’addanci ta Nigeria, ƙarƙashin Ofishin Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, da Hajiya Amina, daga Ofishin Ministan Harkokin Mata, da kuma manyan jami’an gwamnatin Jihar Zamfara, ciki har da Kwamishinan Matasa da Wasanni, Hon. Kasimu Yahya Kaura da Sakataren Dindindin na Ma’aikatar, Alhaji Nasir Kaura Galadima da kuma Daraktan Matasa, Alhaji Aliyu Sani.

Daga Bisani an yaba da gudummawar masu bayar da shawara kan harkokin kasuwanci, ciki har da Dr. Ezekiel Bissan, Mataimakin Darakta na Abuja Business School, sai kuma Dr. Olumide Ojo, ƙwararre a fannin tattalin arzikin karkara da birane daga Georgia State University da kuma Victoria Ikani, ƙwararriya kuma masaniya a fannin kididdigar kuɗi da haraji da masana fasaha daga Investornaire Academy sai ƙwararrun masu gina zaman lafiya da sauran masu ruwa da tsaki da su ka taka muhimmiyar rawa wajen nasarar wannan shiri.

An shirya komai domin fito da sabbin shuwagabannin da za su tabbatar da cewa kasuwancin matasa shi ne ginshiƙin samar da zaman lafiya, ƙarfafa haɗin kan al’uma da kuma kawo sauyi mai ɗorewa a fannin tattalin arziki.

 Ku ci gaba da bibiyar shafukanmu na sada zumunta, kuma ku danna kararrawar sanarwar samun sabbin shirye-shiryenmu da zarar an dora, domin samun rahotanni na musamman da sabbin bayanai kai tsaye.

#Arewa #Bugebuge TheHustleRealityShow #BugeBuge #TheHustleNG #PeaceThroughProsperity #ArewaInnovation #EUinNigeria #SearchForCommonGround #YouthEmpowerment #HustleBootcamp2026 #AbujaBootcamp

Share:

Related Articles